Home Taska ‘Yan Ta’addan ISWAP Sun Kai Hari Karamar Hukumar Damboa da ke Jahar...

‘Yan Ta’addan ISWAP Sun Kai Hari Karamar Hukumar Damboa da ke Jahar Borno

‘Yan Ta’addan ISWAP Sun Kai Hari Karamar Hukumar Damboa da ke Jahar Borno

Yan ta’addan ISWAP sun kai hari kauyen Sabon-Gari da ke karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.

Maharan sun halaka manoma 11 ciki harda mace a farmakin wanda suka kai a ranar Asabar.

Kauyen Sabon-Gari na a kimanin kilomita 125 daga garin Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.

Borno – Daily Trust ta rahoto cewa mayakan kungiyar ta’addanci ta ISWAP ta kashe akalla manoma 11 a yayin wani farmaki da ta kai yankin kudancin jihar Borno.

An tattaro cewa ISWAP ta kai mamaya kauyen Sabon-Gari da ke karamar hukumar Damboa ta jihar a ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairu.

Kauyen Sabon-Gari na a kimanin kilomita 125 daga garin Maiduguri, babbar birnin jihar.

A cewar wata majiya ta tsaro, an gano kimanin gawarwaki bakwai a ranar Asabar sannan aka sake samun wasu hudu a ranar Lahadi.

Rahoton ya kuma kawo cewa wata majiya ta kuma bayyana cewar harda mace a cikin mutanen da aka halaka.

Majiyar ta ce:

“Mun gano gawarwakin manoma 11, duk an harbe du ne sau da dama, an binnesu daidai da koyarwar addinin Islama.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp