Home SIYASA Abubuwa 5 da Yasa Mai Mala Buni ya Rasa Jagorancin APC

Abubuwa 5 da Yasa Mai Mala Buni ya Rasa Jagorancin APC

Abubuwa 5 da Yasa Mai Mala Buni ya Rasa Jagorancin APC

Wasu gwamnonin APC sun yi nasara wajen sauke Mai Mala Buni daga shugabancin jam’iyya na kasa.

Ana zargin gwamnan na jihar Yobe da aikata wasu laifuffuka da-dama, daga ciki akwai kin shirya zabe.

A karshe tsohon sakataren na APC ya rasa kujerarsa kamar yadda ta faru da Oyegun da Oshiomhole

A wannan rahoto, Legit.ng Hausa ta kawo dalilai da ake zargin sun taimakawa Mai Mala Buni wajen rasa jagorancin APC na rikon kwarya da yake yi tun 2020.

1. Kin shirya zabe

Babban zunubin da ake tuhumar Mai Mala Buni da aikatawa shi ne ya ki shirya zaben shugabannin jam’iyya na kasa, kwamitinsa ya yi ta daga lokacin zabe.

A matsayinsa na shugaban rikon kwarya da gudanar da zabe, ya kamata a ce Buni ya rike jam’iyya ne na gajeren lokaci, sai a zabi cikakkun shugabanni na kasa.

2. Neman jawowa APC matsala

Irinsu Gwamna Nasir El-Rufai su na ganin an yi amfani da Mai Mala Buni wajen yi wa APC barazana, har an kai ta kara domin a dakatar da shirya zaben shugabanni.

Gwamnonin na APC su na tunanin tun da kwamitin CECPC bai dauki wani mataki ba, ‘yan takarar APC za su iya rasa kujerunsu ko da sun samu nasara a zaben 2023.

3. Harin takara a 2023

Wasu su na da ra’ayin cewa abin da ya sa Gwamna Mala Buni ya yi ta jan lokaci tun Yunin 2020 har zuwa yanzu shi ne saboda harin takarar mataimakin shugaban kasa.

Rahotanni sun ce ana zargin Buni yana neman shugabancin kasa a karkashin APC, har ta kai yana tunanin sauka daga kujerar gwamnan idan zai zama shugaban APC.

4. Zawarcin Jonathan

Akwai masu zargin cewa Mala Buni da mutanensa ne suke kokarin jawo tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan cikin jam’iyyar APC da nufin a ba shi tikitin takara.

Sakataren rikon kwarya na jam’iyya na kasa watau Sanata John Akpanudoedehe ya taba nuna hakan, har ya bayyana cewa shigowar Jonathan za ta amfani APC kwarai.

5. Jawowa APC kowane tarkace

Mala Buni ya yi kokari wajen ganin wasu daga cikin gwamnonin adawa sun sauya-sheka zuwa APC. A haka ne jam’iyyar APC ta karbe Zamfara, Ebonyi da Kuros Riba.

Sai dai kuma bayan zargin zawarcin Jonathan, gwamna Buni ya shigo da irinsu Femi Fani-Kayode cikin APC, wanda hakan sam bai yi wa wasu ‘ya ‘yanta dadi ba.

An yi waje da shi – El-Rufai

Ku na da labari cewa Gwamna Nasir El-Rufai ya ce da an biyewa Mala Buni, watakila duka ‘yan takarar APC a 2023 za su iya rasa kujerunsu kamar yadda aka yi a Zamfara.

El-Rufai ya ce boyayyan nukiliya aka shirya domin a ruguza zaben shugabanni, don haka suka yi bakin kokarinsu wajen ganin an yi waje da Buni tun da ya ki daukar mataki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HURIWA ta Soki Ƴan Sanda da NDPC Kan Jinkirin Binciken Zargin Kutse da aka yi wa Bayanan NIPSS da ya Shafi Jami’in Sojan RuwaƳa'yan El-Rufai Sun Shiga Rikici Yayin da Bashir ya Zargi Bello da Shan Muggan Kwayoyi da Cin Amanar suTsaro, Fafutuka da Nauyin Tabbatarwa Daga Mukhtar Ya’u MadobiONSA ta Fitar da Faɗakarwar Tsaro, ta Bukaci Ƴan Najeriya su ƙara Yawan Tsawaita TsaroHukumar DSS ta Dakatar da Shari'ar Sowore Kan Laifukan Intanet Har Sai Bayan Zaben Shugaban Kasa na 2027Gwarzo ya ba da Gudummuwar ₦10m ga Horarwa na Musamman na PRNigeria Bayan ya ba da Gidansa na Abuja Don Cibiyar Koyon Aikin Jarida2027: Bayan Takardu da Sauran Tsoffin Maganganu Marasa Amfani, ‘Yan Najeriya Sun Cancanci Kamfen Din da Ya Dace Da Matsaloli  Daga Kabir AkintayoGwamnati Tarayya ta Bayyana Bas 100 Masu Amfani da Wutar Lantarki Don Rage Wa Ma’aikatan Gwamnati Matsalar SufuriƳan Ta’adda na Amfani da Kafafen Sada Zumunta da Dandamalin Aikin Tura Kuɗi Don Tallafa Wa Ayyukansu — BukartiBinciken Gaskiya na PRNigeria: Ta Karyata Da’awar Tony Elumelu ta Cewa An yi Satar Man Fetur Kashi 97% Kafin Zamanin TinubuMeyasa Mutuwar Bazata Take Daukar Masu Alheri ta Bar Mugaye ? Na Yushau A. ShuaibSojoji Sun Kama Bindigar AK-103 Da Aka Boye a Cikin Jakar Gero, Sun Kama Mutum Uku A ZamfaraSojoji Sun Kama Shahararren Shugaban Ƴan Bindiga, 'Sanusi Maigilas' a Dajin Katsina2027: Yadda Zan Magance Rashin Tsaro, In Magance Matsalolin Tattalin Arziki da Zamantakewa a Kwara — Zakari MohammedLabarin NIPSS Mai Damuwa: Lokacin da Jami'in Sojan Ruwa Ya Cin Zarafin Mawallafi Daga Nuhu Mohammed
X whatsapp