Home Taska Hukumar Kwastam ta Kama Motar Dangote Makare da Shinkafar Waje 250

Hukumar Kwastam ta Kama Motar Dangote Makare da Shinkafar Waje 250

Hukumar Kwastam ta Kama Motar Dangote Makare da Shinkafar Waje 250

Hukumar kwastam a Najeriya ta yi nasarar cafke wata motar Dangote makare da shinkafar waje.

Hukumar ta bayyana kame motar dauke da buhuna 250 na haramtacciyar shinkafar ta kasar waje.

Hakazalika a wani yankin hukumar ta kame wasu haramtattun kayayakin da suka hada da fatan jaki, ganyen wiwi da sauransu.

Legas – Kwantrolla Janar na Kwastam, Team A Unit, Mohammed Yusuf, ya ce jami’an hukumar sun kwace wata motar babban Dangote makare da buhun shinkafa na kasar waje 250 da aka haramta shigo da su.

Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Ikeja, Legas, yayin taron manema labarai inda ya bada jawabin ayyukan da suka yi cikin makonni hudu a sassa daban-daban, The Punch ta ruwaito.

Ya bayyana cewa a cikin kayan da aka kwace akwai kwantena ta katako mai tsawon kafa 20; buhunan shinkafa masu nauyin 50kg guda 1000; taya na gwanjo guda 3,143; kunshin tufafin gwanjo 320; Buhun fatar jaki 44 da ganyen wiwi kilogiram 137.3.

“Ina farin cikin bayyana cewa cikin makonni hudu, tawaga ta Strike Force Team A, ta karbi N648,300,986 a matsayin haraji. Ta kuma kwace kaya da kudin harajinsu ya kai N373,629,700.

“Ina son in jadada cewa ba mu daukan aiki da wasa musamman aiki mai muhimmanci irin wannan. Masu fasakwabri da ke tunanin za su yi amfani da wannan damar su yi mummunan aikinsu za su sha mamaki,” in ji shi.

Mai magana da yawun sashin, Peter Duniya, ya tabbatar da cewa an kama motar kamfanin Dangote dauke da haramtatun kayan.

“Motar kamfanin Dangote na daya daga cikin kayayyakin da muka kama,” ya kara.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanciGwamnatin Najeriya da gwamnonin APC sun bai wa ƴan kasuwar Singer tallafin biliyan 8Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin majalisar Amurka na hukunta KwankwasoSojojin Najeriya sun daƙile hare-haren mayaƙan ISWAP a BornoFarfesa Abdullahi Pakistan ya bayyana dalilinsa na ajiye shugaban Hukumar NAHCONMajalisar Najeriya ta kafa kwamitin nazari kan gyaran dokar zaɓeRundunar sojin Najeriya ta tura dakaru na musamman zuwa Filato don daƙile ƴanbindigaMajalisar Dinkin Duniya da Turkiya sun yi Alla-wadai da harin da aka kai KwaraAmurka ka iya sake kai Hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci- TrumpAmurka ka iya sake kai hari Nijeriya muddin aka ci gaba da kashe kiristoci
X whatsapp