Home Taska Sojan Najeriya ya harbe Fararen Hula 3 Tare da Raunata Mutane 13

Sojan Najeriya ya harbe Fararen Hula 3 Tare da Raunata Mutane 13

Sojan Najeriya ya harbe Fararen Hula 3 Tare da Raunata Mutane 13

Wani sojan Najeriya da ake zargin yana tu’ammali da miyagun kwoyoyi ya harbe akalla fararen hula uku har lahira kuma ya raunata wasu mutum 13 yayin wani harbin mai-uwa-da-wabi da ya yi.

Wannan al’amarin ya auku ne a tsakiyar garin Mafa da ke jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Ganau sun ce cikin wadanda sojan ya halaka, akwai wata yarinya ‘yar shekara uku, sannan sauran mutum 13 na asibiti inda ake kula da su saboda raunukan da suka samu daga harbin da ya yi musu.

Wani rahoto ya ce sojan na cikin sojojin Najeriya da aka tura yankin domin yakar ‘yan kungiyar Boko Haram da na ISWAP.

Shaidu sun kuma ce an yi nasarar kwace bindigar daga hannun sojan kuma a halin yanzu yana hannun hukumomin soji.

Sai dai rundunar sojojin Najeriya ba ta ce uffan ba dangane da al’amarin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp