Home Taska ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojojin Nijar 6

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojojin Nijar 6

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Sojojin Nijar 6

 

An kashe sojojin Nijar shida wani hari da ƴan bindiga suka kai kudu maso yammacin ƙasar, kusa da iyaka da Burkina Faso, kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta sanar ranar Asabar.

Harin wanda aka kai a ranar Alhamis, shi ne na biyu cikin kwanaki 10 da ke nuna dawowar hare-hare a yankin bayan shafe makwanni ba a kai hari ba.

Sanarwar ma’aikatar tsaron ta ce “Wasu gungun ƴan ta’adda ɗauke da makamai sun yi wa ayarin sojojin Nijar kwanton ɓauna a kusa da kauyen Kolmane.”

Sanarwar ta ce sojoji shiga aka kashe yayin da ɗaya ya samu rauni da kuma mota da aka lalata. Babu ƙarin bayani kan makomar maharan.

Yankin Tallaberi ya sha fama da hare-hare musamman a yankunan da ke kan iyaka da Burkina Faso da Mali inda mayaƙa masu iƙirarin jihadi masu alaƙa da Al Qaeda da IS ke kai hare-hare.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp