Adadin Mutanen da Suka Rasa Rayukansu a Harin Jirgin Kasar Abuja-Kaduna

Adadin Mutanen da Suka Rasa Rayukansu a Harin Jirgin Kasar Abuja-Kaduna

Wata majiya a kusa da tsahar jirgin ƙasa dake Rigasa Kaduna ta ce ana tsammanin fasinjoji Bakwai suka mutu a harin.

Tuni dai hukumar sufurin jiragen ƙasa ta kasa ta dakatar da jigila a hanyar biyo bayan harin da yan ta’adda suka kai wa jirgin.

Wani Fasinja da ya tsira ya bayyana cewa maharan sun zagaye Jirgin bayan sun ta da Bam, suka buɗe wa mutane wuta.

Kaduna- Aƙalla mutum Bakwai ake fargabar sun rasa rayukan su a harin Bam da yan bindiga suka kai kan hanyar jirgin ƙasa ta Abuja-Kaduna jiya da daddare.

Wata majiya kusa da tashar jirgin dake Rigasa a Kaduna tace mutanen kuma fasinjojin jirgin sun mutu ne yayin harin, wasu kuma sun ɓata yayin da yan ta’adda suka tasa wasu

Hukumomin masu alaƙa da lamarin na kokarin haɗa kai da hukumar sufurin jirgaen kasa ta ƙasa (NRC) domin gano bayanan Fasinjojin da abun ya shafa, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Manajan hukumar NRC, Mista Fidet Okhiria, tun da farko ya tabbatar da kai harin ga manema labarai, smma bai bada cikakken bayani ba.

Yadda lamarin ya faru

Wani Fasinja da ya tsira daga harin, ya gaya wa yan jarida ta wayar Salula cewa suna tsaka da tafiya, “Muka ji wata ƙara Buuuum, Bam ya tashi.”

Ya kuma iya tuna wasu abubuwan da suka faru, inda ya ce:

“Ƙasa ta girgiza, yayin da idanuwa suka fara ganin giftawar harsasai, ƙarar bindiga ta mamaye wurin.

A cewarsa, Fasinjojin jirgin da suka kai kusan dubu ɗaya, sun faɗa kan juna yayin da taragon jirgin ya sauka daga kan hanya.

Ya ƙara da cewa yan ta’addan sun zagaye jirgin, sannan suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, kuma mutane da dama sun jikkata sanadin haka.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 9 hours 47 minutes 4 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 11 hours 28 minutes 29 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here