Rikicin Rasha da Ukraine: Kada Wanda ya ci ko Sha Wani Abu a Wajen Taron Neman Zaman Lafiya – Ministan Ukraine
Ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytro Kuleba, ya bai wa mahalarta taron tattaunawar da ake yi da Rasha shawara cewa kada wanda ya ci ko ya sha wani abu a wajen.
Ministan ya ba da shawarar ce gabanin fara taron da za a yi a Turkiyya.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Kafar yada labaran Ukraine ce ta bayyana hakan inda ta ce ministan ya bada shawararce bayan zargin da aka yi cewa an bai wa shahararren attajirin nan Roman Abramovich guba a farkon tattaunawar zaman lafiyar da aka yi a farkon watan nan.
Akwai shakku a kan zargin da ake a kan zargin bai wa Mr Abramovich guba, inda wani jami’a a Amurka da ba a bayyana sunansa ba ya shaida wa kamfanin dillancin na Reuters cewa ba mamaki canjin yanayi ne ya shafi Mr Abramovich.
A ci gaba da tattaunawar ta yau a kan rikicin Rasha da Ukraine, Abramovich ya isa wajen a cewar kafar yadda labaran Turkiyya.












