Jagoran jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, kuma Dan Takarar Shugabancin Qasa karkashin Inuwar Jam’iyyar, Bola Ahmad Tinubu yace Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osibanjo ba Dan sa bane.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a yammacin ranar Litinin a Birnin Tarayya Abuja, jim kadan bayan kammala ganawar sa da Gwamnonin Jam’iyyar APC su 12.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ganawar da aka yi a masaukin Gwamnan Jihar Kebbi, a Asokoro dake Birnin tarayya Abuja, ta zo bayan Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osibanjo ya bayyana Kudirin sa na tsayawa takarar Shugaban Kasa a kakar zaben shekarar 2023.
Da aka tambaye shi don yin tsokaci dangane da Takarar Mataimakin Shugaban Kasar, wanda ake masa kallon dansa ne a siyasance, Tinubu yace “Bani da wani da da ya girma da zai iya yin Takarar shugaban kasa, “Bani da wani Da daya girma zai iya wannan furuci.
Sai dai yace ya ganawa da gwamnonin jihohin ne domin neman hadin kai, goyon baya da karfafa Gwuiwa dangane da burin sa na tsayawa takarar shugabancin Nijeriya a shekarar 2023.












