Home Labarai Dakarun ‘Yan Sanda Sun Lakadawa Kwamandan Hukumar NSCDC Duka

Dakarun ‘Yan Sanda Sun Lakadawa Kwamandan Hukumar NSCDC Duka

Dakarun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Imo dauke da Makamai, sun kutsa shalkwatar hukumar tsaro ta Civil Defence (NSCDC) inda suka lakadawa kwamandan hukumar Micheal Ogar dukan kawo wuka.

Rahotan da PrNigeria ta samu ya nuna cewa tuni jami’an ‘Yan Sandan suka halaka mai tsaron lafiyar Kwamandan, bayan da Dakarun Hukumar ta Civil Defence ke kwance cikin muggana raunika.

PRNigeria ta rawaito cewa jami’an ‘Yan Sandan Kwantar da tarzo ta Mobile Police na Squadron – 18 a Jihar ta Imo ne suka aika ta wannan danyen hukunci.

Lamarin dai ya faru ne bayan da kwamandan ya shiga tsakanin wata takaddama daga auku tsakanin jami’in hukumar da wasu jami’an ‘Yan sanda.

Wata sahihiyar majiya ta shaidawa PRNigeria cewa lamarin ya faru tsakanin jami’an inda aka dingi musayar wuta da manyan bindigu a shalkwatar hukumar ta NSCDC dake kusa works layout a Owerri, Babban Birnin Jihar.

Binciken da PrNigeria ta gudanar ya nuna cewa rikicin ya samu asali ne bayan takaddama  mai zafi tsakanin direban kwamandan Hukumar ta NSCDC na  Jihar ta Imo da wani Dan Sanda a kayan gida wanda ya rufe hanyar da kwamandan zai wuce.

Har zuwan lokacin hada wannan rahoto, PRNigeria bata sami nasarar jin ta bakin Kakakin hukumomin guda biyu ba

By PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp