Babban mai tace labarai na jaridar PRNigeria, Yusha’u Shuib ya rasa mahaifin sa Shiek Abdulhameed Agaka mai kimanin shekaru 77 a duniya.
Sheik Abdulhameed, sananne addinin islama ne kuma babban limamin garin Agaka dake karamar hukumar Ilorin da yamma dake jihar kwara, ya koma ga mahaccinsa sakamakon wata gajiriyar rashin lafiya a ranar asabar.
Tunu aka gudanar da jana’idar sa kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a ranar lahadi a gidan sa dake garin na Agaka.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
An haifi malamin a zuri’ar Imam Shuaib Said, mashahurin malamin addini, kuma masanin Al’kurani mai tsarki jagoran addinin muslunci a garin na Agaka.
Babban limamn na Agaka yayi karatun sa a makarantar School for Arabic Studies wato (SAS) dake jihar Kano daga bisani ya tafi Jami’ar Bayero dake jihar ta kano inda ya sami babban Digiri a fannin ilimin Alqur’ani a da kuma Nahawun Harshen Larabci.
Shaihin malamin a lokuta da daban-daban ya kasance shugaban sashen Nazarin harshen larabci a kwalejin ilimin addinin Musulunci da shari’a ta kano wato Aminu kano College of legal and Islamic studies.
Fatan Allah ya gafarta masa ya kuma inganata abinda ya bari yasa Aljanna ce makomar sa.












