Home General Ana cigaba da zaman makokin Jami’an Tsaron da ‘Yan Bindiga suka Hallaka...

Ana cigaba da zaman makokin Jami’an Tsaron da ‘Yan Bindiga suka Hallaka a jihar kaduna

A wani hari da ‘yan bindiga suka kai yankuna biyu na karamar hukumar Birnin Gwari na jihar Kaduna, ‘yan bindiga sun halaka jami’an tsaro da dama a yankin.

Rikicin ya samo asali ne, bayan jami’an tsaro sun kashe wani yaro makwanni uku da suka gabata, wanda yake kulawa ‘yan bindigan shanunsu.

Wannan ne ya sa ‘yan bindigar daukar fansa a ranar Litinin kan yankunan da mummunan lamarin ya auku na Kubau da Anguwan Zakara

‘Yan bindiga sun salwantar da rayukan jami’an tsaro da dama a yankuna biyu da inda suke cin karensu babu babbaka na karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, kamar yadda.

Daga cikin jami’an tsaron da suka rayukansu sun hada da; jami’an NSCDC, ‘yan sanda, soji da kuma wasu ‘yan sa kai a ranar Lahadi, kamar yadda majiyar ta bayyana.

“Ba ranar Lahadi bane suka fara harin, sai dai sun fara ne kwanaki hudu da suka wuce. An kai hari titin Funtua zuwa Birnin Gwari, inda jami’an tsaro da dama suka rasa rayukansu. Amma na ranar Lahadi, ‘yan sa kai biyu, ‘dan sanda daya da wani soja sun rasa rayukansu.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp