Home General Akwai ‘Yan Siyasa da ke Aiki Tukuru Wajen Ganin Sun Bata Sunan...

Akwai ‘Yan Siyasa da ke Aiki Tukuru Wajen Ganin Sun Bata Sunan Yusuf Bichi – DSS

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bayyana cewa, akwai wani shiri da wasu gurbatattutun ‘yan siyasa ke yi na ganin sun bata sunan babban daraktanta, Yusuf Bichi da wasu manyan jami’anta.

Wannan na na kunshe  ne a cikin wata sanarwa da kakakin DSS, Peter Afunanya ya fitar, inda yace wasu ‘yan siyasa a ciki da wajen gwamnati na kokarin kawo cikas ga aikin hukumar na tsayawa tsayin daka ga dakile barna.

Afunanya ya kuma ce ‘yan siyasan Najeriya na amfani da kungiyoyin farar hula da kungiyoyi masu zaman kansu wajen bata sunan Bichi ba gaira ba dalili.

Hukumar ta DSS ta ce ya kamata ‘yan kasa su guji duk wani batu da ke ake yi na ganin an shafa bakin fenti ga manyan jami’anta, musamman daraktan.

Kafafen yada labarai na bata sunan Bichi, inji hukumar DSS

Hakazalika, sanarwar ta zargi wasu gidajen jaridu da kafafen yada labarai da kirkirar rubuce-rubuce da ke bata sunan Bichi da ahalinsa a kwanakin nan.

Saboda haka, hukumar tace tana zuba ido, kuma za ta dauki matakin da ya dace a lokacin da ya dace kan masu yada bayanan karya game da hukumar, kuma ta ce babu abin da zai hana aiwatar da ayyukanta.

“Hukumar DSS, don haka na fatan sanar da jama’a da su kaucewa wadannan batutuwa kuma su yi watsi da duk wani bakin fenti da ake son shafawa katarin DG.”

Hakazalika, Afunanya ya ce, hukumar za ta ci gaba da tunkarar duk wata barazana ta tsaron kasa tare da aiki tukuru wajen tabbatar da an yi zabe cikin lumana.

Yadda batutuwa suka taso game da DG na DSS

A baya kadan, kungiyoyin farar hula a Najeriya sun tada magana cewa, hukumar ta DSS na kokarin tarfa gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele bisa zargin ta’addanci, The Guardian ta ruwaito.

Baya ga haka, kungiyar kiristoci ta CAN ta ce akwai hannun ‘yan siyasa wajen kitsa kwamushe gwamnan babban bankin na CBN.

Ana ta yada cewa, batun kama gwamnan n CBN na da alaka da siyasa tun bayan da bankin ya ba da umarnin sauya fasalin kudi tare da sanya sabbin ka’idojoji ga kashe yawon kudi a kasar.

Hakazalika, an yi ta cece-kuce game da yadda ake zargin matar shugaban na DSS ta umartar cin zarafin dan takarar gwamnan NNPP a jihar Kano.

PRNigeria hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp