Home General ‘Yan sanda a kano sun kubutar da yaran da akayi garkuwa dasu...

‘Yan sanda a kano sun kubutar da yaran da akayi garkuwa dasu a jihar

Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta kama wasu matasa guda biyu da ake zargi da garkuwa da wasu Yara guda 2 har suka nemi a tura musu Naira Miliyan 20 a matsayin kudin Fansa.

Cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, yace rundunar ta yi nasarar kama matasan ne lokacin da suka aikowa da Iyayen yaran da suka sace da wasika mai dauke da lambar wayarsu da Kuma account number domin tura musu kuɗin fansa.

Yace Matasa Masu suna Nura Auwal Mai shekaru 22 mazaunin Rijiyar lemo da abokin sa Abubakar Lawan mai shekaru 22 mazaunin Bachirawa a kano sun bukaci a iyayen yaran da su basu Naira Miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa, yayin da daga bisani suka Amince zasu karbi Naira Miliyan 4 kafin su sake su.

Kiyawa yace tuni wadanda ake zargi suka amsa laifin da ake zargin su da aikatawa, kuma kwamishinan ‘yan sandan jihar kano CP Mamman Dauda ya bada umarnin fadada bincike da Kuma gurfanar da su a gaban kotu domin yanke musu hukunci daidai da laifin su.

Kiyawa yace tuni aka ceto yaran wadanda kowannen su bai wuce shekaru 3 zuwa 4 a Wani kango Inda aka ajiye su, bayan sun karbi korafi daga wani Auwal Sale tun a ranar 26 ga watan Janairu 2023.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Kwamitin Bincike Kan Mutuwar Ma'aikatan Haƙar Ma'adinai 37 a Hukumar Kula da Haƙar Ma'adinai ta NSCDCMajalisar Dattawa ta 10 da Ma'anar Jagorancin Majalisa Daga Kabir AkintayoDarakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna Yusuf
X whatsapp