Home General A karo na 3 Buhari ya sake ganawa da Emefiele,

A karo na 3 Buhari ya sake ganawa da Emefiele,

Shugaba Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da Gwamnan Babban Bankin kasar (CBN) Godwin Emefiele a fadarsa da ke Abuja.

Wannan shi ne karo na uku da gwamnan yake ganawa da shugaban tun bayan matsalar karancin takardar kudin kasar na naira da ta bullo a sakamakon sauyin wasu daga cikin manyan takardun kudin na 200 da 500 da kuma 1,000 da Babban Bankin ya yi.

Bayan wannan ganawar tasu ta uku a Aso Villa, Emefiele, ya ki cewa uffan ga manema labarai lokacin da ya fito.

Bugu da kari babu wata sanarwa daga fadar ko wani jami’i na gwamnati da ya bayyana dalilin ziyarar gwamnan bankin zuwa fadar shugaban kasar.

Sai dai duk da haka ana ganin ba za ta rasa nasaba da halin da kasar ke ciki ba na karancin takardun na naira da abin da wahalhalun da al’ummar kasar suka samu kansu a ciki a dalilin canjin.

Ko a ranar laraba da ta gabata shugaban kasar ya gana da gwamnan bankin bayan Kotun Kolin kasar ta dakatar da wa’adin da bankin ya sanya na daina karbar tsofaffin kudin daga ranar 10 ga watan Fabarairu.

Har sai Kotun ta yanke hukunci ranar Laraba da ke tafe, a kan karar da gwamnonin jihohi uku – na Kaduna da Kwara da kuma Zamfara suka shigar a kan batun canjin kudin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Tinubu Zai Bai wa Mazauna Abuja Manyan Ayyuka Kyautar a Watan Disamba – WikeHukumar Kwastam ta Tantance Kusan Mutane 3,000 Yayin da Aikin Daukar Ma'aikata na 2025 ya KareMazauna Kauye Sun yi Murna Yayin da Sojoji Suka Dakile Harin Ta'addanci, Sun Kwato Shanu a SakkwatoFarashin Canji da Yawa ya ja wa Najeriya Asara Fiye da Tallafin Man Fetur – CardosoGwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Kwamitin Bincike Kan Mutuwar Ma'aikatan Haƙar Ma'adinai 37 a Hukumar Kula da Haƙar Ma'adinai ta NSCDCMajalisar Dattawa ta 10 da Ma'anar Jagorancin Majalisa Daga Kabir AkintayoDarakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka Mutu
X whatsapp