Hukumar zaben Najeriya, INEC, ta ce za ta adana muhimman kayan zaben 2023 a Babban Bankin kasar, bayan da a baya ta ce ba za ta yi hakan ba.
Idan dai ba a manta ba a 2022 sakamakon damuwa da jama’a da kungiyoyi suka nuna da kuma matsin lamba da aka yi wa hukumar ta INEC, kan adana kayan a CBN, bayan da Gwamnan bankin Godwin Emefiele ya nuna sha’awarsa ta yin takarar shiugabancin kasar, hukumar ta nuna cewa ba za ta ajiye kayan a can ba.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Shugaban hukumar zaben Farfesa Mahmood Yakubu, a ranar 4 ga watan Yuni 2022, ya ce ba za a kai muhimman kayan zaben CBN ba.
A ranar Talata ne Kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu zabe na hukumar ta INEC Festus Okoye ya bayyana cewa wasu daga cikin muhimman kayan zaben suna Babban Bankin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Okoye ya ce yuni hukumar ta samar tare da kai muhimman kayan zaben kamar su takardar rubuta sakamako da takardar zabe kuma ta adana su a bankin inda daga can za ta kai su ofisoshin INEC da ke kananan hukumomin kasar.
PRNigeria hausa












