Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta jingine shirinta na yin ƙarin kuɗin wutar lantarki da kashi 40 cikin 100 cikin wata mai zuwa.
Cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Joe Ajaero, ya fitar, ya ce matakin zai ƙara wa ‘yan ƙasar musamman talakawa ”wahalhalu da matsin da suke ciki”.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Kafofin yaɗa labaran Najeriya sun ruwaito hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta kasar NERC na shirin ƙara kuɗin wutar daga ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa.
A wani mataki na janye tallafin da gwamnatin ƙasar ke biya kan kudin wutar lantarkin.
BBC ta tuntuɓi hukumar ta NERC, don jin bahasinta kan matakin, to amma jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Michael Faloseyi ya ce ba a ba shi izinin yin magana kan batun ba.
‘Yan ƙasar da dama sun bayyana kaɗuwarsu kan matakin ƙarin kuɗin wutar lantarkin, suna masu fargabar cewar zai haifar musu da ƙarin matsin tatalin arziki.
A watan da ya gabata ne gwamnatin ƙasar ta sanar da matakin janye tallafin man fetur, lamarin da ya haddasa ƙaruwar farashin man fetur da na kayan abinci a faɗin ƙasar.
PRNigeria hausa












