An rantsar da gwamnan Ondo na riƙo, Lucky Aiyedatiwa a matsayin cikakken gwamnan jihar, sa’o’i kadan mutuwar Rotimi Akeredolu sanadin cutar kansar jini .
Mataimakin gwamnan, ya karɓi ragamar mulkin jihar a matakin riƙo, bayan Gwamna Rotimi Akeredolu ya aika wasiƙa ga majalisar dokokin jihar don sanar da ita game da ƙudurinsa na tafiya jinya da kuma miƙa ragamar mulkin jihar ga Lucky Aiyedatiwa.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Alƙalin alƙalan jihar Mai shari’a Olusegun Odusola ne ya rantsar da shi a ofishin gwamnan Ondo dake ciki birnin Akure.
Idan za’a Iya Tunawa Dai tun da farko, an yi ta dambarwa a fagen siyasar jihar, lokacin da majalisar dokokin Ondo ta fara yunƙurin tsige Lucky Aiyetadiwa daga kan kujerar mataimakin gwamna.
Sakataren gwamnan jihar da kwamishinonin Ondo da shugaban jam’iyyar APC da alƙalan jihar na cikin manyan jami’an da suka halarci taron rantsuwar.
PRNigeria hausa












