Rahoyanin daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa mataimakin Shugaban hukumar hana fasa kwari ta Kasa dake lura da harkokin kudi da gudanarwa Essien Etop Andrew ya yanke jiki ya fadi a gaban zauren Majalisar wakilan Nijeriya.
A yayin da yake amsa tambayoyin a gaban ‘yan majalisar wakilan Andrew ya sarke, wannan ne ya sanya shi faduwa kasa magashiyyan.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa masu bayar da agajin gaggawa na majalisar sun garzaya da shi asibiti amma abin yaci tura ya kai ga mutuwar sa.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ta cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun majalisar wakilan Akin Rotimi, ya fitar ta ce majalisar zata bayar da gudunmawar don ganin an fahimci lamari da abinda ke kewaye da shi ga dukkanin masu ruwa da tsaki.
Haka kuma ta ce kakakin majalisar Tajuddeen Abbas, ya mika sakon ta’aziyyar sa ga iyalai da hukumar ta NCS, yace majalisar ta damu matuka da mutuwar jami’an
Bamidele Salam wanda shike jagorantar Kwamitin dake bincike ya ce kwamitin ya dage zaman zuwa mako guda domin girmama marigayin.
PRNigeria Hausa











