Gwamnan jihar Kano ya sanar da janye dokar hana fita da ya saka sakamakon tarzomar da ta biyo bayan zanga-zanga kan matsin rayuwa a Nijeriya.
Abba Kabir Yusuf ya sanar da matakin ne yayin da yake yi wa ‘yanjarida jawabi a jihar yau Litinin bayan wata ziyarara gani da ido da ya kai harabar kotun da matasa suka yi barna a ranar zanga-zangar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
“Gwamnati ta janye wannan doka gaba ɗaya, kuma mai girma gwamna ya jinjina wa malamai da jami’an tsaro da suka jajirce don ganin an samu zaman lafiya,” kamar yadda Kwamashinan Yaɗa Labarai Baba Halilu Dantiye ya shaida wa manema labarai cikin wani saƙon murya.
Gwamnati ta saka dokar a ranar 1 ga watan Agusta bayan wasu ɓata-gari sun auka wa gine-gine da shagunan mutane tare da yin wawashe kayayyaki a ranar farko ta zanga-zangar.
PRNigeria Hausa












