Home Labarai Mayakan Boko haram 44 sun mika wuya a jihar Borno

Mayakan Boko haram 44 sun mika wuya a jihar Borno

Dakarun rundunar sojin Nijeriya ta sami nasarar hallaka ýan ta’addan masu yawa, yayin da da dama suka mika wuya ga dakarun, haka kuma sun sami nasarar kwato Bindugu, alburusai, bama-bamai, da kuma garken shanu, gami da kama wadanda ake zargin ‘yan ta’addan ne a wani samume da suka kai.

Ta cikin wata sanarwa da PRNigeria ta samu rundunar ta ce a ranar 12 ga watan agustan 2024, ta kai wani simame a maboyar mayakan kungiyar tayar da kayar baya na boko haram tsagin ISWAP a karamara hukumar Bama dake jihar Borno a Arewa maso gabashin kasar.

Inda dakarun ta suka sami nasarar bindigar kakkabo jirgin sama ta (RPG) bama-bamai, bindugu guda biyu kirar gida, kwanson alburushi bindiga kira AK47, Babura guda 6 da kuma wasu magunguna kala-kala.

Haka kuma ayankin na arewa maso gabashi wasu mayakn boko haram 44 da iyalansu sun mika wuya a kananan hukumomin Dikwa da Gwoza dukka a jihar ta Borno.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Kwamitin Bincike Kan Mutuwar Ma'aikatan Haƙar Ma'adinai 37 a Hukumar Kula da Haƙar Ma'adinai ta NSCDCMajalisar Dattawa ta 10 da Ma'anar Jagorancin Majalisa Daga Kabir AkintayoDarakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna Yusuf
X whatsapp