Home General Gwamnatin Nijeriya ta musanta karin harajin kayayyaki a kasar

Gwamnatin Nijeriya ta musanta karin harajin kayayyaki a kasar

Gwamnatin Nijeriya ta musanta raɗe-raɗin cewa ta ƙara yawan harijin kayayyaki zuwa kashi 10%, daga kashi 7.5%.

Ministan kuɗi na Najeriya, Wale Edun a cikin wata sanarwa ya ce har yanzu dokokin ƙasar sun ƙayyade cewa hariji kayayyakin da ake biya kashi 7.5% ne.

Ya ce: “Harajin kayayyaki a Nijeriya yana nan a kashi 7.5% , kuma hakan gwamnati ke karɓa. Domin haka gwamnati da dukkan hukumomin ta suna biyayya ga wannan tanadi na doka, kuma ba za su saɓa ba.

Rahotan da aka riƙa yaɗawa game da ƙarin harajin kayyakin a Nijeriya ya janyo martani daga ɓangarori da dama, ciki harda na ƴan siyasa.

Tuni dai tsohon mataimakin shugaban ƙasar kuma ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya yi allawadai da matakin.

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sada zumuntansa na X.

Ya bayyana matakin a matsayin wani abu da zai yi mummunar illa ga al’ummar Najeriya, yana mai hasashen cewa hakan zai kara ta’azzara matsalar tsadar rayuwa da ƙasar ke fama da ita da kuma kawo cikas ga ci gaban tattalin arzikin Nijeriya.

“Ƙara kuɗin haraji zai zama wuta mai zafi da za ta cinye ainihin mutanenmu.” in ji Atiku.

“Wannan matakin zai haifar da koma baya da ƙara zurfafa matsalar tsadar rayuwa a cikin gida da kuma ƙara tabarbarewar ci gaban tattalin arzikin ƙasar ne kawai”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp