Rahotannin daga birnin tarayya Abuja na tabbatar da cewa jami’an hukumar Tsaro ta DSS sun mamaye ofishin kungiyar SERAP da ke birnin.
wannan dai na zuwa ne bayan da jami’an suka kama shugabn kungiyar kwadago ta kasa Joe Ajero.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Rahotannin sun nuna cewa jami’an sun nemi ganawa da shugabannin kungiyar kare hakkin dan Adam da lura da al’amuran tattalin arziki.
A cikin wani rubutu da aka wallafa a shafin X na SERAP, an bayyana cewa jami’an DSS sun mamaye ofishinsu ba bisa ka’ida ba.
Kungiyar ta bukaci Shugaban kasa Tinubu da ya gaggauta umartar DSS da ta daina tsoratarwa da cin zarafin ‘yan Najeriya.











