Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce wahalhalu da “sadaukarwar” da ‘yan ƙasar suka yi ba su tashi a banza ba tun bayan hawa mulkinsa a watan Mayun 2023.
Da yake bayani cikin saƙonsa na sabuwar shekara da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Tinubu ya ce sabuwar shekarar “za ta kusanta mu da kakkyawar Najeriya da muke ta hanƙoro”.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A cewarsa: “Gare ku ‘yan ƙasa, sadaukarwar da kuka yi cikin wata 19 da suka wuce ba ta tashi a banza ba. Ina tabbatar muku cewa kuma ba za ta tashi a banza ba nan gaba. Mu ci gaba da aikin gina ƙasa tare.”
Tinubu ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta ƙara mayar da hankali wajen aiwatarwa da kuma “bijiro da sauye-sauyen da suka zama wajibi” domin haɓaka tattalin arzikin Najeriya.












