Home General Ya kamata Tinubu ya janye ƙudurin dokar haraji – NLC

Ya kamata Tinubu ya janye ƙudurin dokar haraji – NLC

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, NLC ta buƙaci shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya janye ƙudurin dokar haraji da ya gabatar ga majalisar dokokin ƙasar domin bayar da dama kan sake yin nazari.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin saƙonta na sabuwar shekara, wanda shugabanta Joe Ajaero ya fitar a yau Laraba.

Saƙon ya ce “domin samar da tsarin dimokuraɗiyya mai tabbatar da ci gaban ƙasa, dole ne mu gina tsari kan tubalin tattaunawa, da bai wa masu ruwa da tsaki damar tsoma baki a harkar gina ƙasa.

“A kan haka ne muke sake yin kira ga gwamnatin tarayya da ta janye ƙudurin harajin da yanzu haka ke a gaban Majalisar dokoki domin bai wa duk ɓangarorin da suka dace bayar da gudumawa a kansa”.

Sanarwar ta ce ƙungiyar, ita ma za ta so ta taimaka wajen samar da kyakkyawan tsarin haraji wanda zai samu karɓuwa a tsakanin al’umma, kuma ya taimaka wajen ci gaban ƙasa.

Batun ƙudurin harajin da Tinubu ya gabatar, na daga cikin manyan sauye-sauyen da sabon shugaban ƙasar ya bijiro da su tun bayan hawa mulki a shekara ta 2023.

Sai dai ƙudurin harajin ya fuskanci turjiya daga ɓangarori da dama na ƙasar, ciki har da Majalisar tattalin arziƙi ta ƙasar, da gwamnoni da kuma ƙungiyoyi.

Lamarin da ya tursasa wa Majalisar dokokin ƙasar jinkirta muhawara kan ƙudurin, yayin da shugaban ƙasar ya buƙaci ma’aikatar shari’a ta ƙasar ta haɗa hannu da majalisar domin warware ɓangarorin dokar da ake ganin su ne suka haifar da taƙaddama.

Sai dai a tattaunawarsa da kafafen yaɗa labaru sa’ilin hutun ƙarshen shekara a birnin Legas, wadda ita ce ta farko tun bayan hawa kan mulki, Tinubu ya sha alwashin tabbatar da ganin sabuwar dokar harajin ta fara aiki.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Shugaban Kwastam, Adeniyi ya Lashe Kyautar IPRA ta Musamman a Greece, ya Kuma Yaba da Nasarar da Najeriya ta Samu a Gasar Grand PrixSojoji Sun Ceto Mutane 14 da Aka yi Garkuwa da su, Sun Kwato AK-47 da Alburusai a Katsina2027: Dalilin da Yasa Atiku ya Saka El-Rufai a Cikin Tawagar Yaƙin Neman Zaɓe - MomoduObi Zai Rasa Goyon Bayana Idan Ya Karɓi Tayin Mataimakin Shugaban Ƙasa – UtomiHukuncin Kotun Koli ba Zai Shafi Takarar Gwamna ta ba – Sanata BubaObi ya Ajiye Kudi Don Samun Riba Yayin da Jama'a Ke Shan Wahala — Gwamnatin AnambraKotu ta Tabbatar da Pantami a Matsayin Ɗan PDP, ta Umurci Sabon Zaɓen Fidda Gwani a GombeDaga Hannun Masu Garkuwa Zuwa Tsira: Shugaban Bungudu ya Kubuta, Sojoji Sun Kwato ShanuTsohon Shugaban Tsaron Google ya yi Gargaɗi Kan AI Zai Iya Cutar wa Mafi Girma ga Yara Fiye da Kafafen Sadarwa Na ZamaniNIMC ta Karyata Da'awar Bayyana Bayanan NINMutane 4 da ake Zargi da Hakar Ma'adanai ba Bisa Ka'ida ba Sun Mutu Sakamakon Ruftawar Rami a FilatoBa na jin Haushin Waɗanda Suka Watsar da ni - El-RufaiSojoji Sun Kama Masu Haƙar Ma'adinai ba Bisa Ka'ida ba Sun Kwato Kayan Aiki a Jihar NasarawaZaɓen 2027: IGP Disu ya Umarci Manyan Jami'ai da su Ƙarfafa Leken Asiri, da Shirye-shiryen Aiki2027: Ƙungiyar TMG ta Bukaci Atiku, Obi, Makinde, Sowore Su Tattauna Kan Ɗan Takara Ɗaya na Hadin Kai
X whatsapp