Home Labarai Gwamnan Abba ya karrama wasu fitattun Kanawa 35

Gwamnan Abba ya karrama wasu fitattun Kanawa 35

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karrama wasu mutum 35 ’yan asalin Jihar Kano waɗanda suka yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa.

A sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24 ya ce daga cikin waɗanda gwamnan ya karrama akwai janar-janar ɗin soji 19, Farfesoshi 6 da wasu fitattun Kanawa 10.

An bayar da lambobin yabon ne ga fitattun mutanen maza da maza a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da ya gudana a Fadar Gwamnatin Kano ranar Asabar da daddare.

Abba ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da haɗa gwiwa da waɗannan zaƙaƙurai domin tabbatar da haɗin kai, zaman lafiya da kuma ci gaban Jihar Kano.

Gwamnan ya kuma hori matasa masu tasowa da su ɗauki waɗannan fitattun mutane a matsayin madubi wajen karkatar da alkalar rayuwarsu a fannonin ilimi daban-daban domin ɗaga martabar Kano a nan cikin gida da ƙetare.

Daga cikin waɗanda aka karrama akwai mace ta farko a Arewacin Nijeriya da ta zama Farfesa a fannin likitancin mata da ƙananan yara da mace ta farko a matsayin Kwamishinar ’Yan sanda da kuma Bakano kuma ɗan Nijeriya na farko da ke riƙe da muƙamin Shugaban Ƙungiyar Injiniyoyi ta Duniya.

A nasa jawabin, Shugaban Limaman Nijeriya, Sheikh Nasir Muhammad Adam, ya ƙalubalanci waɗanda aka karrama da su kasance alƙiblar da za ta zama haske ga matasa masu tasowa kafin cikar wa’adinsu a ban ƙasa.

Fitattun Kanawan da aka karrama sun haɗa da Air Marshal Hassan Bala Abubakar, Manjo-Janar M S Ahmed, Manjo-Janar IS Ali, Manjo-Janar A M Garba, Manjo-Janar Sani Sumaila Ibrahim, Manjo-Janar B U Yahya, Manjo-Janar S Y Bashir, Manjo-Janar U B Abubakar, Manjo-Janar Faruk Mijinyawa da Manjo-Janar Jamal Abdulsalam.

Sauran sun haɗa da Air Vice Marshal M Yusuf, Air Vice Marshal G A Bello, Air Vice Marshal B R Mamman, Air Vice Marshal SK Usman, Air Vice Marshal M S Ibrahim, Air Vice Marshal KM Umar, Rear Admiral Abdullahi Ahmad, Rear Admiral Aliyu Gaya da Rear Admiral Idi Abbas.

Ragowar waɗanda suka samu karrramawar sun haɗa da Farfesa Shehu Ahmad Said Galadanci, CON, Dokta Nasiru Sani Gwarzo, Yakubu Adamu Kofar Mata, DIG Dasuki Galadanchi, DDG DSS, Alhaji Ado Muazu, Farfesa Umma Abdullahi, Farfesa Hadiza Galadanci, Farfesa Nazifi Abdullahi Darma, Farfesa Hamisu Armayau Bichi, Farfesa Sagir Adamu Abass da Kwamishinar ’Yan sanda, CP Hajiya Hauwa Ibrahim.

Akwai kuma Rislanuddeen Muhammad, Injiniya Mustafa Balarabe Shehu, Arc. Hauwa Hassan Tudunwada, Ado kabiru Minjibir Mni da kuma Marwan Mustapha Adamu mni.

Bikin ya samu halarcin dattawa da kuma fasihai a fannonin rayuwa daban-daban daga garin na Kano.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Kwamitin Bincike Kan Mutuwar Ma'aikatan Haƙar Ma'adinai 37 a Hukumar Kula da Haƙar Ma'adinai ta NSCDCMajalisar Dattawa ta 10 da Ma'anar Jagorancin Majalisa Daga Kabir AkintayoDarakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna Yusuf
X whatsapp