Home General Rasuwar Galadima: Gwamnan Kano ya mika ta’aziyyarsa ga shugaban APC Abdullahi Abbas

Rasuwar Galadima: Gwamnan Kano ya mika ta’aziyyarsa ga shugaban APC Abdullahi Abbas

Gwamnatin jihar Kano ta mika sakon ta’aziyya ga mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, Majalisar Masarautar Kano da kuma Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alh. Abdullahi Abbas da sauran iyalai, bisa rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi.

Marigayi Galadiman Kano, wanda ya rasu yana da shekaru 91 a daren ranar Talata a Kano, ya kasance fitaccen dattijo kuma jigo a masarautar Kano. Ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa Masarautar, ya rike manyan mukaman sarauta da suka hada da Wamban Kano, ya kuma taka muhimmiyar rawa a Masarautar a karkashin marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya sanyawa hannu kuma raba manema labarai a jihar Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana wannan rashin a matsayin babban rashin, ba wai ga Masarautar kadai ba har ma da jihar da daukacin al’ummar Kano baki daya

Gwamna Abba Kabiru ya yaba da kyawawan halaye na Marigayi Galadiman Kano, a matsayinsa na mutum mai kishi da jajircewa wajen kiyaye al’adun Kano.

Bugu da kari, gwamnan ya jajantawa daukacin al’ummar jihar Kano, bisa babban rashi na Alhaji Abbas Sanusi. Ya kuma yi addu’ar Allah ya jikansa da rahama ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi.

Gwamna Yusuf ya bukaci al’ummar Kano da su rika sanya marigayi Galadiman Kano a cikin addu’o’insu don neman masakuma kiyaye kimar hadin kai da hidima da ya tsaya a kai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HURIWA ta Soki Ƴan Sanda da NDPC Kan Jinkirin Binciken Zargin Kutse da aka yi wa Bayanan NIPSS da ya Shafi Jami’in Sojan RuwaƳa'yan El-Rufai Sun Shiga Rikici Yayin da Bashir ya Zargi Bello da Shan Muggan Kwayoyi da Cin Amanar suTsaro, Fafutuka da Nauyin Tabbatarwa Daga Mukhtar Ya’u MadobiONSA ta Fitar da Faɗakarwar Tsaro, ta Bukaci Ƴan Najeriya su ƙara Yawan Tsawaita TsaroHukumar DSS ta Dakatar da Shari'ar Sowore Kan Laifukan Intanet Har Sai Bayan Zaben Shugaban Kasa na 2027Gwarzo ya ba da Gudummuwar ₦10m ga Horarwa na Musamman na PRNigeria Bayan ya ba da Gidansa na Abuja Don Cibiyar Koyon Aikin Jarida2027: Bayan Takardu da Sauran Tsoffin Maganganu Marasa Amfani, ‘Yan Najeriya Sun Cancanci Kamfen Din da Ya Dace Da Matsaloli  Daga Kabir AkintayoGwamnati Tarayya ta Bayyana Bas 100 Masu Amfani da Wutar Lantarki Don Rage Wa Ma’aikatan Gwamnati Matsalar SufuriƳan Ta’adda na Amfani da Kafafen Sada Zumunta da Dandamalin Aikin Tura Kuɗi Don Tallafa Wa Ayyukansu — BukartiBinciken Gaskiya na PRNigeria: Ta Karyata Da’awar Tony Elumelu ta Cewa An yi Satar Man Fetur Kashi 97% Kafin Zamanin TinubuMeyasa Mutuwar Bazata Take Daukar Masu Alheri ta Bar Mugaye ? Na Yushau A. ShuaibSojoji Sun Kama Bindigar AK-103 Da Aka Boye a Cikin Jakar Gero, Sun Kama Mutum Uku A ZamfaraSojoji Sun Kama Shahararren Shugaban Ƴan Bindiga, 'Sanusi Maigilas' a Dajin Katsina2027: Yadda Zan Magance Rashin Tsaro, In Magance Matsalolin Tattalin Arziki da Zamantakewa a Kwara — Zakari MohammedLabarin NIPSS Mai Damuwa: Lokacin da Jami'in Sojan Ruwa Ya Cin Zarafin Mawallafi Daga Nuhu Mohammed
X whatsapp