Shugaba Bola Tinubu ya nuna ɓacin-rai da kuma kaɗuwa kan kashe mutane da wasu ƴan bindiga suka yi a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.
Shugaban ya yi Alla-wadai da lamarin, ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar jihar – inda ya buƙaci a nemi hanyar warware rikicin da kuma samar da zaman lafiya.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga ya fitar, inda Tinubu ya nanata muhimmancin haɗin-kai ba tare da nuna bambacin addini ko kabila.
“Dole ne shugabannin al’ummomi da na addini da kuma siyasa su zo su haɗa-kai don daƙile waɗannan hare-hare da suka addabi jama’a,” in ji Tinbu.
Aƙalla mutum 50 ne suka mutu a harin da ƴan bindigar suka kai jihar a cikin daren Litinin.










