Ikirari: Wani rubutu da ya karade kafafen sada zumunta na zamani da kuma wasu rahotannin kafafen yada labarai sun yi ikirarin cewa wata mata mai kimanin shekaru 22 a duniya mai suna Zainab Muhamadu na fuskantar hukuncin kisa a jihar Zamfara, bisa zargin sauya addininta daga Musulunci zuwa Kiristanci.
Rahotanni sun ce wani mai hidimar ƙasa (NYSC) da aka ce ana kiransa Fasto Samuel, ya rinjayi Zainab ta sauya addininta bayan sun kulla dangantaka ta ruhi da juna.
Jaridar The Guardian ta wallafa labarin da taken: “Zamfara Woman Faces Death Penalty for Converting to Christianity.” Wato wata ‘yar Zamfara na fuskantar hukuncin kisa bisa Sauya Addini.
Lamarin ya jawo cece-kuce daga masana harkar shari’a da masu rajin kare hakkin ɗan adam, wadanda suka bayyana lamarin a matsayin take hakkin dan Adam, musamman na ‘yancin addini da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.
Tabbatar da Sahihancin Ikirari: Domin tantance sahihancin ikirarin, PRNigeria ta duba rahotanni daga kafafen yada labarai masu inganci. Sai dai, bayan The Guardian, wasu ‘yan kafafen labarai ne kadai suka wallafa irin wannan labari, kuma daga bisani wasu ciki har da Sahara Reporters sun goge labarin, lamarin da sanya shakku kan gaskiyar lamarin.
Read Also:
Bincike ya kara bayyana cewa Gwamnatin Jihar Zamfara ta fitar da sanarwar karyata wannan rahoto. Bisa ga rahoton jaridar Politics Digest, wanda bai ma wallafa labarin ba, gwamnatin ta bayyana ikirarin a matsayin “ƙarya kuma mai ɗauke da ruɗani,” tana zargin masu yada labarin da ƙoƙarin tayar da rikicin addini.
Shaidu: PRNigeria ba ta samu wata shaida ta gaskiya da ke nuna cewa an kama ko ana shari’a da wata mai suna Zainab Muhamadu a gaban kotun Shari’a a Zamfara ba.
Har ila yau, hoton da aka haɗa da labarin da ke yawo an gano cewa na wata mata ce mai suna Aalia Reeves, wata ‘yar asalin Amurka wadda ke ƙirƙirar abubuwan da suka shafi Musulunci a kafar TikTok.
Aalia ba ta taɓa zuwa Najeriya ba, balle a ce tana da alaƙa da jihar Zamfara ko wani lamari na sauya addini.
A cikin bidiyonta na TikTok, Aalia ta yi bayani yadda kishinta da sadaukarwarta ga addinin Musulunci ya taimaka wajen kyautata fahimtar mahaifiyarta Kirista game da addinin.
Kammalawa: Duk da yaduwar wannan labari da kuma wallafa shi da wasu kafafen yada labarai, babu wata shaida mai tushe ko tabbatacciya da ke nuna cewa akwai wata Zainab Muhamadu da ake tuhuma ko shari’a da ita a jihar Zamfara saboda sauya addini.
Hakanan hoton da ke cikin rahoton ba na Zainab ba ne, sai dai an dauki hoton Aalia Reeves domin ƙarfafa ƙaryar labarin.
Hukunci: labarin na Ƙarya ne, Babu wata shaida da ke nuna cewa gwamnatin Jihar Zamfara ta gurfanar da wata Zainab Muhamadu bisa sauya addini. Wannan ikirari ba shi da tushe, balle makama ya ta’allaka ne da ƙarya da satar hoto. Don haka, ƙaryane.
Daga PRNigeria