Wasu rahotannin sun bayyana cewa an kashe musu mutum 20 sakamakon harin ‘yan bindiga da kuma farmakin da wani jirgin sojin Najeriya ya kai domin fatattakar ‘yan bindigar.
Al’ummar wasu ƙauyuka da ke yankin ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, sun ka bayyana hakan kamar yadda bbc ta rawaito.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun sace mutune sama da 50 da ke aikin noma, amma jirgin saman da ya kawo dauki ya kashe wasu daga cikin ‘yan sakai da ke ƙoƙarin korar ‘yan bindigar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Mazauna unguwar Mani da ke yankin ƙaramar hukumar ta Maru sun ce ‘yan bindigar waɗanda suke kan babura sun kai musu harin da rana a lokacin da ake tsaka da aikin gona.
Mutanen sun ce koda isarsu sai suka fara harbin kan mai uwa da wabi da kuma kama wasu mutanen.











