Gwamnan jihar Neja da ke tsakiyar Neja ya nemi aikin haɗin gwiwa da matatar man fetur ta Dangote domin haƙowa da kuma hada-hadar ɗanyen mai da aka gano a Tekun Bida da ke jihar.
Umar Bago ya bayyana aniyar gwamnatin tasa ne yayin wani jawabi da ya yi a bikin baje-kolin kasuwanci da aka gudanar a Minna babban birnin jihar ranar Lahadi.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa kamfanin na Dangote ne ya ɗauki nauyin bikin.
Gwamnan ya siffanta albarkatun ɗanyen man da aka gano jihar na da shi a matsayin tikitin “cigaban tattalin arzikin Neja”.
NAN ya ruwaito cewa wani bincike da aka gudanar a 2023 ne ya gano rijiyoyin mai 17 da za a kasuwancinsa a jihar, inda aka ƙiyasata cewa za a iya kasuwancinsa na tsawon shekara 70.












