Ina da ƴancin Mu’amala da Kowa ba Tare da La’akari da Jam’iyya ba – Wike
Ministan Abuja Nyesom Wike ya bayyana cewa shi ko kaɗan ba ya irin siyasar nan ta ƙiyayya da adawa mai zafin gaske da ke iya hana zumunci.
Ministan ya bayyana haka ne a matsayin martani ga masu sukar ziyarar da ya kai wa shugaban APC, Farfesa Nentawe Yilwatda.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya ce yana da ƴancin mu’amala da kowa ba tare da la’akari da jam’iyya ba, sannan ya ƙara da cewa ba dole ba ne sai ya bayyana abin da suka tattauna a ziyarar wadda ya bayyana ta abota.
Ya ce alaƙar da ke tsakaninsa da shugaban na APC ba ta yau ba ce, inda ya ƙara da cewa sun yi aiki tare a lokacin da shugaban na APC yake riƙe da muƙamin minista.
Wiƙe ya ƙara da cewa shi babban abin da ke gaban shi bai wuce ya sauke nauyin a ke gaban shi, inda ya ƙara da cewa ayyukan da yake yi a zahiri suke.












