Home SIYASA Bayan Tsige ‘Yan Majalisa 20: ‘Yan Sanda Sun Mamaye Harabar Majalisar Dokokin...

Bayan Tsige ‘Yan Majalisa 20: ‘Yan Sanda Sun Mamaye Harabar Majalisar Dokokin Jahar Cross River

Bayan Tsige ‘Yan Majalisa 20: ‘Yan Sanda Sun Mamaye Harabar Majalisar Dokokin Jahar Cross River

An tsaurara matakan tsaro a harabar majalisar dokokin jihar Cross River.

Hakan ya biyo bayan tsige yan majalisa 20 da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi a ranar Litinin kan sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Jami’an yan sanda na sashi daban-daban ne suka karbe majalisar tun daga karfe 6:00 na asuba.

Cross River – Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa sashi daban-daban na rundunar yan sandan Najeriya sun karbe dukka hanyoyin da ke sada mutum ga harabar majalisar dokokin jihar Cross River.

Sun mamaye wuraren ne tun da misalin karfe 6:00 na asubahi kamar yadda shaidu suka bayyana.

Sashin yan sandan da ke kasa sun hada da na yaki da garkuwa da mutane, masu yaki da kungiyar asiri da kuma jami’an yan sanda na yau da kullum, dukkansu dauke da makamai.

The Sun ta kuma rahoto cewa an hangi wasun su na cikin harabar majalisar dokokin.

An kuma gano wasu daga cikin jami’an yan sandan tsaye kusa da ofishin Gwamna Ben Ayade wanda bai da nisa da wajen.

A daya bangaren majalisar akwai filin wasa na UJ Esuene Stadium Calabar. An kuma gano wasu mutane da ake zaton magoya bayan jam’iyyar siyasa ne suna zukar hayaki da shan lemuka masu zafi.

Masu ababen hawa da masu wucewa na fuskantar matsala wajen kutsawa cikin cunkoson jami’an tsaro da motocinsu.

An tattaro cewa an tsaurara matakan tsaron ne biyo bayan hukuncin da mai shari’a Taiwo Taiwo ya yanke a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja inda ta kori ‘yan majalisar jihar 18 da kuma wasu ‘yan majalisar wakilai guda biyu kan sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar All Progressives Congress.

Jam’iyyar APC mai mulki ta yi ikirarin cewa ta shigar da kara kotu domin a dakatar da aiwatar da hukuncin, yayin da jam’iyyar ta garzaya zuwa kotun daukaka kara.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp