Home Labarai TSARO: Dakarun MNJTF Sun Sake Halaka Kwamandan Mayakan ISWAP da Mayakan Kungiyar...

TSARO: Dakarun MNJTF Sun Sake Halaka Kwamandan Mayakan ISWAP da Mayakan Kungiyar 15

Dakarun Rundunar Sojin Hadin Gwuiwa MNJTF sun sami nasarar halaka mayakan kungiyar tada kayar baya ta Boko Haram tsagin ISWAP, Abu Fatima da wasu Karin Mayakan Kungiyar 15, a wani gagarunmin hari da suka kai maboyar mayakan a yankin Tafkin Chadi.

A ranar 9 ga Afrilun, 2022 jirgin yaki samfurin Super Tucano bisa sarrafawar Rundunar Sojin Sama karkashin Dakarun na MNJTF da kuma dakarun Mi35 hadi da dakarun Mi171 sukayi barin wuta kan dabar mayakan na ISWAP dake a arewacin Jubularam a Karamar Hukumar Marte dake jihar Borno.

Wani jami’in liken asiri ya shaidawa PRNigeria cewa an kai harin ne ta sama bayan wasu bayanan sirri da aka samu kan cewa kwamandan na ISWAP na Shirin yin fito na fito da Dakarun Sojin, nan rundunar sojin  ta dauki matakin kai harin.

Kwamandan Mayakan na ISWAP Abu-Fatima na da mayaka 500 a karkashin sa, kuma shike lura da yankunan Kirta Wulgo, Sabon Tumbu, Kwaleram, Sigir da Jibularam, Abbaganaram da Yarwa Kura.

Majiyar ta shaida cewa kwamandan ya jagoranci mabanbanta hare haren da aka kaiwa dakarun sojin Najeriya a garuwan da dama ciki har da Kukawa, Abadam, Malam Fatori duk a karamar hukumar Marte.

Zafafa hare-haren da dakarun sojin ke yi ta sama wanda COIN ke jagoranta, ya sanya mayakan na Boko Haram tsagin ISWAP neman mafaka a yankin riversbanks dake tsakanin Nijeria da jamhuriyar Niger.

Sabbin mabuyar ‘Yan kungiyar ta ISWAP sun hadar da Lumburam, Fiyoo, Lada da Jarwaram, dukkan su a yankin na riverbanks.

Wata majiya ta shaidawa PRNigeria cewa a ranar 11 ga Afrilu an shigo da wasu makamai da suka hadar manyan bindigun Atilare cikin garin Tudun Wulgo da mashigar Bakkassi dake kasar Kamaru.

A yayin wata huduba salar juma da guda cikin kwamandojin kungiyar ta ISWAP ya gabatar a Sabon Tumbu, bukaci mayakan kungiyar su sake jajircewa wajen kare Daular daga farmakin soji.

Dakarun sojin hadin gwuiwar karkashin Operation lake and Desert sanity, na cigaba da kai hare-hare kan maboyar ‘yan ta’addar da suka hadar da cikin surkukin daji kan Tsaunuka, ruwa da dukkan maboyan ‘yan ta’addar da suka addabi yankin Arewa maso gabashin Nijeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp