Home Labarai Sojan Nijeriya ya Halaka Kansa Bayan da ake Zargin Sa da Hadin...

Sojan Nijeriya ya Halaka Kansa Bayan da ake Zargin Sa da Hadin Baki

Sojan Nijeriya ya halaka kansa bayan da ake zargin sa da aiki tare da mayakan kungiyar tada kayar baya ta Boko Haram tsagin ISWAP.

PRNigeria ta gano cewa jami’an liken asiri na rundunar sojin Nijeriya ne suka gano Sojan na guda cikin bataliyar sojojin Nijeriya dake Arewa Maso Gabashin kasar, kuma yana da hannu a wasu hare-haren da aka kai a jihar Yobe a makwannin da suka gabata.

Manyan hafsoshin sojin kasar sun fara sa ido kan sojan ne bayan da aka kai wasu hare-hare biyu a garuruwan Geidam da Gashua na jihar ta Yobe, kuma daga nan suka fara bibiyar wuraren da yake zuwa cikin sirri.

An kuma kama shi yayin da yake kokarin tserewa, bayan da ya gane cewa dubunsa ta cika.

Sai dai sojan – wanda kwararre ne wajen sarrafa makamai – ya kwace wata bindiga a hannun daya daga cikin sojojin da ke rakiyarsa kuma ya kashe kansa duk da cewa an saka masa ankwa a hannu.

A makon jiya wasu wadanda ake zargi mayakan ISWAP ne suka kai wani hari kuma suka kashe akalla mutum goma, ciki har da mata.

By PRNigeria Hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp