Home Labarai Kwamandan Sojoji Ya Bace Bayan Dakarun Sojoji Sun Kashe Mayakan ISWAP Da...

Kwamandan Sojoji Ya Bace Bayan Dakarun Sojoji Sun Kashe Mayakan ISWAP Da Dama A Jihar Taraba.

Dakarun Sojin Nijeriya sun sami nasarar halaka wasu da ake zargin ‘ya’ya kungiyar tada kayar baya na Boko Haram ne tsagin ISWAP a Jihar Taraba kamar yadda jaridar PRNigeria ta rawaito.

Mayakan na Kungiyar ta ISWAP sun gamu da ajalin nasu ne a yayin da suka farwa sojojin dake wani samame a Kauyen Tati dake Karamar Hukumar Takum a Jihar.

Sai dai wani rahato ya bayyana cewa Kwamandan dake jagorantar bataliya ta 93 yayi batan dabo kama yadda Jarida ta PRNigeria ta ruwaito.

A kalla Sojoji 6 ne suka rasa rayukan su yayin artabun, sai dai rahoton yace sojin sun sami nasarar halaka ‘yan ta’addan masu tarin yawa.

Wata majiya daga Rundunar Sojin ta tabbatar da cewa an nemi Kwamandan da guda cikin masu taimaka masa an rasa, duk da dai sojojin a yain musayar wutar sun sami nasarar halaka ‘yan bindigar da dama.

“ta cikin wasu mabambanta hare-hare da sojojin suka kai sun sami nasarar halaka mayakan ISWAP a kauyen Ananum dake Donga a wani shinge da kuma mararraba bisa taimakon wasu dakarun sojin.

By PRNigeria

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp