Kungiyar ta da kayar baya ta Boko Haram tsagin ISWAP, sun hallaka tsohon mataimaki na musamman ga Abubakar Shekau, bayan yayi kokarin mika wuya.
Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa mayakan na ISWAP sun halaka Abu-sadiq Burbur, bisa zargin sa da shirin mika wuya ga Dakarun Rundunar Sojin Nijeriya.
Wata Majiya mai tushe ta shaidawa PRNigeria cewa an halaka Burbur ne a kauyen Galta da ke kusa da Madagali bayan kungiyar ISWAP ta tuhume shi da laifin cin amanar kasa.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
inda daga bisani aka gurfanar da shi a wata kotun masu tada kayar dake zaman ta a dajin Sambisa wadda Ya-shaik guda cikin mayakan na ISWAP ke jagoranta.
Burbur dai tsohon mashawarci ne ga tsohon shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar shekau.
Ana dai kallon wannan lamari na mika wuya da mayakan na kungiyoyin tada kayar bayan ke yi a ‘yan tsakanin nan nada nasaba da ruwan wuta gami da farmaki da dakarun sojin ke kai musu babu kakkautawa a maboyar su
By PRNigeria Hausa












