Cin Hanci: EFCC Ta Kame Babban Akanta Janar, Ahmad Idris

Hukumar Yaƙi da Masu Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati a Nijeriya EFCC, ta cafke Babban Akanta Janar na ƙasar Ahmed Idris bisa zargin karkatar da kudade gami da almundahanar Naira Biliyan 80.

Wannan na cikin wata takardar sanarwa da hukumar ta aikowa PRNigeria mai dauke da kwanan watan 16 ga watan Mayun 2022, da kuma sa hannun jagoran sashin yada labaran hukumar Wilson Uwujaren, wadda ke tabbata da damke babban akantan.

Wata majiyar sirri daga hukumar ta shaidawa PRNigeria cewa akntan ya kushi kudaden ne ta hanyar wata haramtacciyar hanya tare da yin amfani da ‘yan uwa da abokan arzikida nufin zuba jari a jihar Kano da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Sanarwar ta kara da cewa hukumar ta kama shine sakamakon kin amsa gayyatar da ta yi masa, bisa zarge zargen al’mundahana.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 29 minutes 56 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 11 hours 11 minutes 21 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com