Home Labarai Gwamnatin Nijeriya Tace Ba za tayi Amfani Da Karfi Ba Wajen Karbo...

Gwamnatin Nijeriya Tace Ba za tayi Amfani Da Karfi Ba Wajen Karbo Fasinjojin Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna Ba

Fadar shugaban kasa tace ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun yaudari Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta hanyar gaza cika Alkawarin da suka dauka duk da cewa gwamnatin tarayya ta biya musu bukatun su.
Mai Magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai.
Garba Shehu yace gwamnatin tarayya ta cika wa jagoran ‘yan ta’addan Alkawarin data dauka na sakin matar sa dake da ciki, amma daga bisani ya karya Alkawarin daya dauka.
Lokacin da suke tattaunawar sulhu da Gwamnatin tarayya, sun yi alkawarin sakin fasinjojin jirgin da suka yi garkuwa dasu amma masu garkuwar sun gaza cika Alkawarin da suka dauka.
Garba shehu yace bayan gwamantin tarayya ta sauki alkawarin data dauka daga bangaren ta, su kuma ‘yan bindigar suka zo da wani sabon salon yaudara.
Wannan dai na zuwa ne sa’oi kadan bayan da shugabanin Nijeriya Muhammadu Buhari ya gana da fasinjojin da ‘yan bindigar suka sako a fadar gwamnatin tarayya a ranar Alhamis.
Garba shehu ya kara da cewa ba wannan karon farko da ‘yan ta’addan ke saba alkawarin da suka dauka ba, amma wannan ne karon farko da gwamnatin tarayya ta bayyana abinda ke faruwa ga Al’ummar kasa tsakanin ta da ‘yan bindigar.
Yanzu haka dai akwai sauran fasinjoji 31 da suka rage a hannun ‘yan ta’addan a daji, amma gwamnatin tarayyar tace baza tayi amfani da karfin tuwo ba domin karbo su, saboda tana bukatar karbo su a raye.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp