Home Labarai Jami’an Tsaron Masar Sun Kama Tukur Mamu a Filin Jirgin Alkahira

Jami’an Tsaron Masar Sun Kama Tukur Mamu a Filin Jirgin Alkahira

Jami’an Tsaron Masar Sun Kama Tukur Mamu a Filin Jirgin Alkahira

 

Alhaji Tukur Mamu, jagoran masu sasantawa tsakanin ‘yan bindiga da fasinjojin da aka yi garkuwa da su daga wani jirgin kasa mai zuwa Kaduna a watan Maris, an kama shi a birnin Alkahira, babban birnin kasar Masar, tare da iyalansa.

Mamu wanda ke kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajji, an tsare shi na tsawon sa’o’i 24 a filin jirgin sama na Alkahira, kuma ana shirin dawo da shi gida Nijeriya.

Da yake zantawa da Aminiya, Mamu ya ce ya bar Najeriya ne a ranar Talata, kuma bayan da jami’an tsaron Masar suka bincike shi, ba a gano wani abu mai laifi a hannunsa ba.

Mamu ya zayyana wani shiri da gwamnatin Najeriya ta yi na tsare shi a wata kasa kamar yadda aka yi wa dan gwagwarmayar ‘yancin Yarbawa, Sunday Igboho, amma hakan bai samu ba saboda gwamnatin Masar din ta gano cewa takardunsa na gaske ne.

Aminiya ta ruwaito Mamu ya fice daga tattaunawar da ‘yan bindigar bayan ya yi zargin cewa gwamnatin Najeriya na yi masa barazana da kuma yunkurin bata masa suna.

Har yanzu gwamnati ba ta mayar da martani kan ikirarin Mamu ba amma wasu na zarginsa da hada baki da ‘yan ta’adda, zargin da ya musanta.

Cikakkun bayanai daga baya…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp