‘Yan Sanda sun Kama Mutumin da ya Damfari Ma’aikatan POS a Anambara
A jihar Anambra, ‘yan sanda sun kama wani mutum da ya damfari ma’aikatan POS
Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta cafke wani mutum mai suna Chisom Nweke, mai shekaru 26, da ake zargi da yin amfani da laya wajen damfarar ma’aikatan POS a Awka da kewaye.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
‘Yan sanda sun kama wanda ake zargin ne a ranar 15 ga watan Satumba da misalin karfe 9 na safe a Amawabia, karamar hukumar Awka ta Kudu a jihar Anambra.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Ikenga Tochukwu ya fitar a ranar Alhamis, ta ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa.
Ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wadanda ake zargin sun yanke farar takarda mai girman kudi tare da ba wa ma’aikatan POS su ajiye.
Tochukwu ya ce ana ci gaba da kokarin cafke sauran ‘yan kungiyar sa.












