Home DUNIYA Sojojin Nijeriya na cigaba da samun Nasarar kan mayan Boko Haram a...

Sojojin Nijeriya na cigaba da samun Nasarar kan mayan Boko Haram a Arewa maso gabashin Kasar

Dakarun sojojin Nijeriya sun sami nasarar kama mayakan boko haram, tare da hallaka wasu a mafa
Rundunar sojojin nijeriya karkashin Dakarun operation hadin kai bisa hadin gwiwa da jami’an sa kai na vigilanti a daren litinin sun sami nasara hallaka mayakan boko haram 8 tare da kama guda a raye a wani harin kwanton bauna da suka gudanar a karamar hukumar Mafa dake jihar Borno a Arewa maso gabashin Nijeriya.
Wannan na zuwa ne bayan da hafsan hafsoshin Sojin Nijeriya Laftanal Janar Farouk Yahaya, ya bukaci dakarun sojin da su sake matsa kaimi wajen kai hare-hare ga ‘yan ta’addan dake cikin dajin Sambisa da kuma yankin tafkin Chadi.
Jaridar PRnigeria ta tattaro cewa dakarun sojin sun sami nasarar kai harin kwanton baunar ne bayan wasu bayanan sirri da suka samu a kauyen Ngoum dake kusa da garin Maiduguri babban birnin jihar ta Borno, hakan ya basu damar fatattakar mayakan.
‘yan ta’addan da dakarun suka hallaka sune wadanda ke aikata fashi da makami a dukkan fadin kananan hukumomin Mafa, jere da kunduga
Dakarun sun sami nasarar halaka 8 daga cikin su tare da kama guda 1 da raia, sai kuma nasarar kwato baburan hawa da kuma bindiga kirar AK47 a cewa PRNigeria.
Haka kuma a wani cigaban wata kungiya daga cikin Al’ummar kauyen kwayam a jihar borno sun sami nasarar halaka wasu ‘yan ta’adda da ake kyautata zaton mayan boko haram ne, a wani harin kwanton bauna da suka gudanar da makamin kwari da baka.
Majiyoyin sun kuma tabbatar da cewa matasan kauyen sun sami nasarar kwato babur din hawa guda daya inda suka mika shi ga hannun dakarun sojojin dake Gwongulan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp