Home General Wasu Sabbin Hare-Haren ‘Yan Bindiga a Jihohin Sokoto da Katsina sun yi...

Wasu Sabbin Hare-Haren ‘Yan Bindiga a Jihohin Sokoto da Katsina sun yi sandiyyar Mutuwar Mutane 13 tare da garkuwa da 73

‘Yan bindiga sun sake hallaka mutane 14, tare da yin garkuwa da 18 a jihohin Sokoto da Katsina dake arewa maso yammacin Nijeriya.

A gabashin jihar Sokoto , an hallaka mutane 13 tare da yin garkuwa da 73 wanda suka hadar da mata da kananan yara.

Hare-haren ya auku a kauyuka mabanbamta, da suka hadar da sabon birni, gada da kuma yankunan karamar hukumar Goronyo.

Jaridar daily ta ruwato cewa an dukkan hare-haren an kai su ne a lokaci gusa ranar litinin din makoon daya gabata.

Da yake tattaunawa da jaridar wani mai rike da sarautar gargajiya a sabon birin, wanda ya bukaci a sakaye sunan sa, ya ce kauyuka 3 mayakan suka kaiwa hari a karamar hukumar sa inda suka hallaka mutane 11.

Kauyukan sun hadar da gatawa da Dangari inda mutane 6 suka mutu, 2 a gatawa 3 kuma a kurawa.

Shugaban jami’an sa kai na Vijilanti a sabonda birni, Musa Muhammad da Dan Majalisa ma wakiltar sabon birnin a zauren majalisar wakilai Mustapha Boza, dake wakiltar Sabon birni ta kudu su bayyana cewa dukkan  mutanen an halaka su ne a gona ranar litinin da karfe 5 na yamma.

Boza yace sun kuma yi garkuwa da mutane da dama yayi da suka kai harin.

Haka kuma shugaban karamar hukumar Goronyo, Abdulwahab Goronyo, wand aya koka bisa harin yace maharani sun hallaka mutane 23, yayin da suka yi garkuwa da sauran a garuruwan shinkafi da  kagara a ranar litinin din data gabata.

shima Dan majalisa mai wakiltar mazabar Gada ta gabas a zauren majalisar jiha, Kabiru dauda, ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane sama da 50 da suka hadar da mata da kananan yara a ranar litinin a yankin.

“bazan iya fada maka takamaiman adadin mutanen da aka sace ba, amma da yawan mutanen mun sun samin raukana, amma dai suka samun kulawar likitoci a asibitocin daban-daban. Kamar yadda ya bayyana.

Dauda ya hakikance cewa duk da korafe-korafen da Al’ummar ke yi bisa harin rashin  tsaron da suke ciki, kawo yanzu babu wani matakin da aka dauka domin magance matsalar ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp