Gwamnatin Jihar Kano cire kwamishinan harkokin addini na jihar Kano, Dr. Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible) daga mukaminsa.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne, ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Asabar a birnin Kano.
Sanarwar ta kara da cewa korar kwamishinan ta biyo bayan halin rashin da’a da yake nuna wa a matsayinsa na ma’aikacin gwamnatin jahar Kano kuma mai rike da mukami, har aka same shi da furta wa su kalamai da ba su yi wa gwamnatin dadi.
Malam Garba ya bayyana cewa, an kuma same shi yana gudanar da al’amuran ofishinsa ba bisa ka’ida ba ta hanyar rage wa rage ranakun zuwa aiki ga ma’aikatansa ba tare da sahalewar gwamnatin ba.
Ya kara da cewa tuni Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya aike wa majalisar dokokin jihar sunan wani da ya zaba wanda zai maye gurbin sa, Dakta Nazifi Ishaq Bichi na Jami’ar Bayero Kano a matsayin sabon kwamishinan Harkokin Addini na jihar Kano.
Sanarwar ta kara da cewa, gwamnan ya yi fatan alheri ga korararren kwamishinan.
Dr. Tahir abaya shi ne kwamishinan addinai kuma wanda ya jagoranci Mukabalar da aka yi da Abduljabbar Nasir Kabara bayan yin wasu kalamai a cikin karatukansa da za su haifar da tunzura al’umma.
bayan kammala mukabalar ce da Abduljabbar Nasir Kabara na gaza kare kansa yasa gwamnatin jahar Kanon ta gurfanar da shi a gaban wata kotu a birnin Kano wadda shafe kusan watanni 15 ana shariar

Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1255 days 1 hour 6 minutes 8 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1237 days 2 hours 47 minutes 33 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021
Report By: PRNigeria.com