Home General Gwamnatin Tarayyar Nijeriya tace Babu Batun Karin Albashin Ma’aikata

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya tace Babu Batun Karin Albashin Ma’aikata

Gwamnatin Tarayya Nijeriya ta ce ba wani shiri da take yi na karawa ma’aikatan ta Albashi kamar yadda aka ruwaito a wasu jaridun kasar a kwanakin baya, inda ta ce wasu “alawus-alawus na musamman” ne kawai take shirin karawa.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da kakakin ma’aikatar, Olajide Oshundun ya fitar, inda ya jaddada cewa babu batun sake yiwa ma’aikata karin Albashi.

Ngige, yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnati a ranar Talata, ya ce kwamitin da shugaban kasa ya kafa kan albashin ma’aikata na yin nazari, kuma ana sa ran zai fito da tsarin daidaita albashin a sabuwar shekara.

Sai dai ministan a ranar Juma’ar nan ya ce  karin da ya yi magana a kai shi kan alawus din wasu ma’aikatan na musamman ba wai karin Albashi ba, inda ya kara da cewa har yanzu ana kan aiki.

Sanarwar ta kara da cewa, “Kwamitin shugaban kasa kan albashi (PCS) ta ofishin sakataren gwamnatin tarayya (OSGF) ya karbi shawarwarin duba alawus-alawus na ma’aikatu da hukumomin gwamnati da dama.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp