Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero ya bukaci al’ummar jihar da su ci gaba da mutunta shugabanni, sannan su yi amfani da kuri’unsu wajen zaben shugabanni na gari a lokacin zabe .
Sarkin ya bayyana haka ne a yayi da ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Apc, Asiwaju Bola Ahmad tunibu a fadar sa dake jihar kano a Arewa maso yammacin Nijeriya.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Cikin sanarwar da sakataren yada labaran Masarautar kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya aikewa manema labarai yace Sarkin wanda ya bayyana Kano a matsayin cibiyar harkokin zabe ya yi kira ga jama’a da su yi amfani da kwarewarsu wajen zaben wadanda za su inganta rayuwar al’umma gaba daya.
Tun da farko dan takarar shugaban kasa Bola Ahmad Tunibu ya ce ya zo jihar Kano ne domin kaddamar da yakin neman zabensa a Arewa maso Yamma kuma ya nemi addu’ar Sarkin da kuma al’ummar jihar.
A yayin ziyarar dan takarar shugaban kasa ya samu rakiyar gwamnan jihar Dr. Abdullahi umar Ganduje, da mataimakinsa Dr. Nasiru yusif Gawuna, gwamnan jihar Zamfara, Sanata Barau Jibrin, shugaban jam’iyyar na jiha Abdullahi Abbas, tsofaffin gwamnoni, da manyan jami’an gwamnatin tarayya.
PRNigeria hausa












