Home General NNPC Tana Tafka Asara Wajen Sayar da Mai Saboda Umarnin Gwamnatin Tarayya...

NNPC Tana Tafka Asara Wajen Sayar da Mai Saboda Umarnin Gwamnatin Tarayya Kan Batun Tallafi – Timipre Sylva

Karamin Ministan Fetur a Najeriya ya ce NNPC tana tafka asara wajen sayar da mai saboda umarnin gwamnatin Tarayya kan batun tallafi.

Timipre Sylva ya shaida hakan ne adaidai lokacin da dillalan man fetur ke cewa suna fuskantar karanci mai lamarin da ka iya sake ta’azzara wahalar man har zuwa watan Yuni, saboda shirin gwamnati na janye tallafi baki ɗaya a wannan watan.

An rawaito ministan na waɗannan kalamai ne a yayin da yake bayyana abubuwan da suka aiwatar tsakanin 2015 zuwa 2023 karkashin mulkin Muhammadu Buhari.

A makon da ya gabata, Ministar kuɗi da tsare-tsare, Zainab Ahmed ta ce gwamnati ta ware naira tiriliyan 3.6 na tallafi fetur zuwa Yunin 2023.

An rawaito Sylva a lokacin zantawa da ‘yan jarida a Abuja, na cewa tallafin babban nauyi ne, sai dai kuma wajibi ne ga NNPC da aka daurawa alhakin tafiyar da harkokin fetur a kasar ta ci gaba da daukar asara.

Gwamnatin Najeriya a ranar Litinin ta bayyana cewa ta zuba hannayen jari a matatun mai hudu da ke shirin soma ayyukansu a sassa daban-daban a faɗin Kasar.

PRNigeria hausa

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp