Hukumar zaɓe a Najeriya (INEC) ta tsawaita wa’adin karɓar katin zaɓe da take raba wa a faɗin ƙasar.

Shugaban Sashen Yaɗa Labarai na INEC, Festus Okoye ya ce an ɗauki matakin ne don bai wa masu kada kuri’a isasshen lokaci na karɓar katin kafin fara jefa ƙuri’a a babban zaɓe na 2023.

“Saboda wannan dalilin, an tsawaita wa’adin karɓar katin zaɓen da kwana takwas,” in ji shi.

“A maimakon 22nd ga watan Janairu, za a ci gaba da karɓa har zuwa Lahadi, 29 ga watan na Janairu.”

INEC ta ce lokacin karɓar katin shi ne 9:00 na safe zuwa 3:00 na yamma a kullum da ga Asabar zuwa Lahadi.

Kazalika, tsawaitawar ta shafi dukkan cibiyoyin karɓar katin a matakin ƙananan hukumomi da mazaɓu .

A ranar 25 ga watan Fabarairu ne za a fara kaɗa ƙuri’a, inda ake sa ran yan kasa miliyan 93.4 million da su ka yi rijistar zaɓe za su zaɓi shugaban ƙasa da ‘yan majalisar tarayya.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 5 minutes 30 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 10 hours 46 minutes 55 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com