Home General WHO- kimanin mutane biliyan biyar na fuskantar gagarumin hatsarin kamuwa da ciwon...

WHO- kimanin mutane biliyan biyar na fuskantar gagarumin hatsarin kamuwa da ciwon zuciya saboda cin abinci mai dauke da kitse

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce, kimanin mutane biliyan biyar na fuskantar gagarumin hatsarin kamuwa da ciwon zuciya saboda cin abinci mai dauke da kitse da ta bayyana a matsayin guba.

A shekarar 2018 ne, Hukumar Lafiyar ta Duniya ta yi roko da a kawar da cimakar da ke dauke da kitse ganin yadda mutane dubu 500 suka yi mutuwar-farar-daya a sassan duniya sakamakon wannan cimakar.

WHO ta ce, kasashen duniya 43 da ke dauke da jumullar mutane biliyan 2 da miliyan 800, sun dauki matakin daina kalace da irin wannan cimakar a kasashensu, amma har yanzu akwai mutanen duniya kimanin biliyan biyar da aka gaza ba su kariya a sassan duniya.

WHO ta ce, Masar da Australia da Koriya ta Kudu, na cikin kasashen duniya da suka yi watsi da gargadinta duk da cewa, su ke kan gaba a jerin kasashen da aka fi samun masu kamuwa da ciwon zuciya skamakon yawan cin abinci mai kitse.

Ana yawan cakuda wannan kitsen a cikin cimaka daban-daban da suka hada da man girki da abincin gwangwani da wasu kunsassun kayan kwalama.

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, irin wannan kitsen na dauke da sinadarin guba mai kisa , kuma ya kamata a daina amfani da shi a abinci.

Kamfanoni dai na sanya kitsen ne da zummar hana abinci lalacewa da wuri, sannan yana da saukin samu fiye da sauran sinadarai masu kara wa abinci tsawon wa’adin lalacewa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp