Home General Jirgin kasa dauke da fasinjoji ya kauce hanya tsakanin Abuja zuwa Kaduna

Jirgin kasa dauke da fasinjoji ya kauce hanya tsakanin Abuja zuwa Kaduna

Shugaban Hukumar Jiragen kasa a Najeriya NRC Inginiya Fidet Okhiria ya tabbatar da faruwar hadarin, to sai dai ya ce suna ci gaba da bincike domin tantance dalilan faruwar lamarin ba.

Wannan hadari dai ya faru ne kasa da mako daya bayan bayan da wani jirgin daukar fasinja ya kauce wa hanyarsa a layin dogon da ya tashi daga Itakpe zuwa Warri a cikin jihar Kogi da ke tsakiyar kasar.

To sai dai wasu bayanai na nuni da cewa ga alama jirgin ya kauce wa hanyarsa ne sakamakon zagon kasa, ko dai daga masu satar kwangiri domin sayarwa ko kuma tsageranci.

Dubban mutane ne ke amfani da jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna a matsayin hanyar sufuri domin zuwa yankin Arewacin Najeriya, duk da cewa watanni 9 da suka gabata, ‘yan ta’adda sun dasa bam wanda ya tarwatse a lokacin da jirgin ke wucewa dauke da fasinjoji kusan 900.

Daga bisani dai ‘yan ta’addar sun yi awun gaba da wasu fasinjojin, yayin da suka kashe wasu a lokacin harin, lamarin da ya tilasta dakatar da jigiliar jiragen kasa a wannan hanya tsawon watanni 8.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Fiye da Kashi 60 na 'Yan Najeriya a Yanzu Suna Rayuwa Cikiin Fatara - IMFGwamnatin Najeriya ta Caccaki Afrika ta Kudu kan Harin da ake yi wa ƴan ƙasartaƳan Bindiga sun Buƙaci Kudin Fansa Kafin Sako Dattijan da Suka je Sulhu a ZamfaraMayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a Kano
X whatsapp