Sarkin Fulanin Dambatta da ke jihar Kano, Alhaji Aminu Bello Sulaiman ya amince da naɗin Amb. Mustapha a matsayin Wazirin ƙasar Dambatta.
Wannan na kunshe ta cikin wata sanarwar naɗin da fadar Sarkin Fulanin Dambatta ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin shirye – shirye Dr. Bello Adamu Namura.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sanarwar ta ce “Bisa dogon nazarin halayenka da kuma la’akari da gudummawarka ga Dambatta, jihar Kano da kasa baki daya, da kuma girmama masarautar Dambatta, Mai girma Sarkin Fulani-Dambatta ya umarci a sanar dakai cewa kana daya gada cikin wadanda ya amince a baka mukamin sarautar WAZIRI a kasar Dambatta“
“Saboda haka an tsara jadawalin shirye shirye da tsare tsaren bikin nadin, wanda da zajar an gama shirye shiryen bikin nadin sarautar, kwamitin tsare tsaren zasu sanar da lokacin da za’ayi bikin nadin da zarar an sa rana”
“A madadin Mai girma Sarkin Fulani, muna tayaka murnar samun warnan sarauta da kuma addu’ar Allah Ya tayaka riko, Ya zama jagora bisa wannan amana da nauyi daya dora maka. Muna kuma fatan za’a bada hadin kai wajen bin umurni da dokokin wannan masarauta”
PRNigeria Hausa












